🌐 AI搜索 & 代理 主页

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 2 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • An kashe sojoji a musayar wuta da ƴanbindiga a Zamfara
  • Mutum 80 da aka sace a jihar Kaduna sun koma gida
  • An gurfanar da mutanen da ake zargin hannu a kisan gillar Yelwata
  • An shirya kama ni a harbe ni a yunƙurin juyin mulkin da aka yi - Janar Musa
  • Falasɗinawa sun fara tsallaka iyakar Rafah bayan shekar biyu a rufe
  • Yadda maciji ya kashe matashiyar mawaƙiya ƴar Najeriya a Abuja
  • Sheikh Usman Kusfa Zaria ya rasu
  • Su wane ne shugabannin Boko Haram da ISWAP a yanzu?

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Babu gudu ba ja da baya kan zanga-zanga a Abuja - NLC

    NLC

    Asalin hoton, NLC

    Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC a Najeriya, sun ce suna nan daram kan ƙudirinsu na gudanar da zanga-zangar da suka shirya yi a gobe Talata.

    Sun ce za su yi zanga-zangar ne domin nuna goyon bayansu ga ma’aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Ƙasar Abuja, waɗanda ke neman a biya musu buƙatunsu.

    Ƙungiyoyin na NLC da TUC sun umarci dukkan rassansu da majalisun jihohi a yankin na Abuja da ƙewaye, da su tabbatar sun halarci zanga-zangar lumana da doka ta amince da ita, wadda aka tsara za ta yi ranar Talata.

    Wannan na zuwa ne duk da cewa rundunar ƴansandan Abuja ta shawarci ƙungiyoyin ƙwadagon da su dakatar da zanga-zangar, bisa dalilan tsaro.

    Sai dai, sakataren tsare-tsare na ƙungiyar ta NLC, Nasir Kabir, ya shaida wa BBC cewa ba su da niyyar sauya matsaya kan ƙudirinsu na gudanar da zanga-zangar.

    "Zanga-zanga ce ta lumana da nuna fushi da ma'aikata za su yi kan zalunci na wannan mutumi wanda yake ganin ya fi ƙarfin kowa. Mu dai bai fi ƙarfin mu ba, muna bayan ma'aikata.

    "Idan ba a biya ma'aikata hakkokinsu ba da alawus-alawus da kuma inganta aikinsu ba, yajin aiki yanzu muka fara babu wanda zai janye," in ji Nasir Kabir.

    Rahotanni na nuna cewa ma’aikatan hukumar gudanarwar babban birnin Abuja, sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani tun a ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata, bisa zargin rashin biyan albashi, da rashin ƙarin girma da kuma lalacewar yanayin aiki.

    Lamarin ya sa hukumar FCDA ta garzaya kotun masana’antu ta ƙasar, inda ta bayyana yajin aikin a matsayin wanda bai halatta ba tare da neman kotun ta hana ma’aikatan yajin aikin, sai dai kungiyoyin NLC da TUC sun sha alwashin tsayawa kai da fata wajen ƙwatowa ma’aikatan hakkokin su.

  3. Falasɗinawa na farko sun tsallaka iyakar Rafah zuwa Masar

    Rafah

    Asalin hoton, AFP

    Falasɗinawa marasa lafiya da waɗanda aka jikkata na farko daga Gaza sun tsallaka cikin Masar ta kan iyakar Rafah, bayan sake taƙaitacciyar buɗewa da Isra’ila ta yi.

    Falasɗinawa 50 ne kawai za su iya fita daga zirin a kullum, cikin rakiyar danginsu fiye da mutum biyu.

    Za kuma a bar ƙarin wasu hamsin su shiga daga ɗaya ɓangaren.

    Dukkansu na buƙatar izini daga Isra’ila da kuma Masar, sannan za su fuskanci matsanancin binciken tsaro daga Isra’ila.

    Mashigar Rafa ita ce kawai hanya ɗaya tilo ta shiga ko fita daga Gaza ga Falasɗinawa.

    Dubbai ne ke cikin tsananin buƙatar kulawar lafiya.

  4. Kenya ta yi gargaɗi kan haɗa manyan furenni soyayya da takardun kuɗi

    Kenya

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Babban bankin Kenya

    Babban Bankin Kenya ya gargaɗi masu sayar da furenni da kantunan sayar da kayan yin kyauta, su guji haɗa manyan furennin soyayya da takardun kuɗi.

    Bidiyo sun bazu a shafukan sada zumunta da ke nuna masu kantuna na shirya furennin ƙawa, da kalmasassun takardun kuɗi masu launuka da daraja iri daban-daban waɗanda aka liƙe da gam kuma aka manne da FIN.

    Babban Bankin ya ce masu yin furennin ƙawar na lalata takardun kuɗin Kenya, don haka suna iya fuskantar ɗaurin shekara bakwai idan aka kama su.

  5. An kaddamar da hare-hare kan mayaƙan IS a Mali

    Mali

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Rundunonin sojin sama na ƙungiyar AES sun ce sun ƙaddamar da tsararrun hare-hare ta sama kuma daidai kan mayaƙan IS a kusa da garin Menaka a cikin Mali, daura da kan iyaka da Nijar.

    Hare-haren na ranar Asabar, su ne na baya-bayan nan a wani lamari na tsananta ayyukan soji a yankin kusurwa uku mai cike da tashe-tashen hankula a Sahel.

    A ‘yan makonnin dai hare-haren masu iƙirarin hihadi sun daɗa tsananta.

    Jami’an ƙungiyar AES ɗin sun ce hare-haren ta sama sun faɗa kan mayaƙan ƙungiyar IS na Babbar Sahara, inda suka lalata ababen hawa da kayayyakin aiki tare da hallaka ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da dama ciki har da rukunin ‘yan bindiga masu tafiya a kan babura.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar na cewa hare-haren na sama sun kuma auka wa ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka suka arce bayan jerin samamen da sojojin Mali suka kai ranar Alhamis a arewacin garin Menaka.

    Hukumomin Mali sun ce masu iƙirarin jihadi fiye da 20 aka kashe a ƙarshen mako.

    Luguden wutan ya zo ne bayan wani ƙazamin kwanton ɓauna ranar Alhamis a Inatabakate arewa da Menaka, lokacin da mayaƙan IS na Babbar Sahara suka kai farmaki kan wani rukunin sojojin Mali da mayaƙan Azawad da kuma sojojin hayan Rasha suna sintiri.

    Harin ya janyo gwabza faɗa tsawon sa’o’i da kuma wani jerin hare-haren ramuwar gayya daga sojojin Mali. A cikin wata sanarwa tun da farko a yammacin Lahadi, Babban hafsan sojojin Mali ya ce an kashe wani babban kwamandan ƙungiyar IS, Abou Alghabas Ichmali.

  6. Fifa ta nemi afuwar Birtaniya kan yi wa ƴan ƙasar shaguɓe

    Fifa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta nemi afuwar Birtaniya, bayan furta wasu kalamai da ke cewa gasar kofin duniya da ta wuce ta daban ce, saboda karon farko kenan da babu wani ɗan ƙasar da aka kama da wani laifi.

    Kalaman Gianni Infantino sun janyo fushi da ɓacin-rai a faɗin Ingila a watan da ya wuce, inda hukumar kwallon kafa ta ƙasar ta kwatanta kalaman da abin da bai kamata ba.

    Shugaban na Fifa ya ce ba a yi kalaman da wata manufa ba ko kuma ɓata wa wani rai.

    Mista Infantino ya kuma kare matakinsa na bai wa shugaban Amurka Donald Trump lambar yabo ta zaman lafiya a watan Disamba, inda ya ce shugaban ya cancanci haka.

  7. Rikicin matasa ya janyo ƙona gidaje da jikkata mutane a Kaduna

    Rikici

    Asalin hoton, AFP

    Aƙalla gidaje biyu ne aka ƙona tare kuma da jikkata shugabannin al'umma bayan wani rikici tsakanin matasa a karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

    Rikicin wanda ya ɓarke a ranar Lahadi zuwa safiyar yau Alhamis, ya faru ne sakamakon saɓani kan ayyukan haƙar ma'adinai, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa jaridar Daily Trust.

    Wani shugaban al'umma, Malam Ahmad Mishigi, ya ce rikicin ya shafi matasan anguwar Mishigi da kuma na anguwar Kudu ne kan batun haƙar ma'adinai.

    "Maganar gaskiya ita ce, rikici ne tsakanin matasa. Ya fara ne sakamakon saɓani kan samun abin saka wa a bakin salati," in ji Malam Ahmad.

    Ya ce saɓanin wanda ya fara a shekarar da ta gabata, ya rikiɗe zuwa tashin hankali tsakanin makwabta, inda lamarin ya munana a ranar Lahadi.

    Ya ce duk irin koƙari da shugabanni suka yi na kwantar da tarzomar abin ya citura, inda aka jikkata wasu daga ciki.

    Sai dai, kakakin ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce tuni aka shawo kan lamarin.

  8. Birtaniya ta kakaba wa mutum goma a Iran takunkumi

    Gwamnatin Birtaniya ta kakaba wa wasu mutum goma a Iran takunkumai, ciki har da ministan harkokin cikin gida da kuma shugabannin ƴansanda saboda zarginsu da hannu wajen murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a baya bayan-nan.

    Takunkuman sun haɗa da ƙwace kadarori, haramta musu tafiye-tafiye da kuma hana su jagorantar kamfanoni karkashin dokar Birtaniya.

    Birtaniyar ta ce waɗanda abin a shafa sun musguna tare da jefa masu zanga-zanga cikin uƙuba.

    An kashe dubban mutane a faɗin Iran a watan da ya gabata, yayin da hukumomi suka yi amfani da ƙarfi wajen daƙile masu zanga-zanga.

  9. NAHCON ta kammala kama masaukin mahajjata a Makkah da Madina

    Hajji

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya, NAHCON ta ce ta samu nasarar kammala kama masaukin mahajjatan ƙasar kafin wa'adin da ƙasar Saudiyya ta saka.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban hukumar kan harkokin watsa labarai, Ahmad Muazu ya fitar a madidin shugabanta.

    A sanarwar, ya ce shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne sanar da kammala duk wani shirye-shirye da suka shafi kama masauki.

    "Najeriya ta samu nasarar kammala kama masaukin ne a Makkah da Madina tun kafin ranar da ƙasar Saudiyya ta ware domin kammala duk abubuwan da suka shafi masaukin mahajjata."

    Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar na aiki ne bisa umarnin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya buƙaci hukumar ta Najeriya ta riƙa kallama shirye-shiryenta kafin wa'adin ƙasar Saudiyya.

  10. Kotu ta aika mutanen da ake zargi da kashe-kashen Benue gidan yari

    kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar umarnin tsare mutum tara - da aka zargi da kashe-kashen Yelwata na jihar Beneu a shekarar da ta gabata - a gidan yarin Kuje.

    Mai shari'a Joyce Abdulmalik ya ce za a ci gaba da tsare su a gidan yarin har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar.

    Babban lauyan gwamnati kuma ministan Shari'ar ƙasar, Lateef Fagbemi (SAN) ne babban mai shigar da ƙara a shari'ar.

    An gurfanar da mutanen tara bisa zarge-zarge 57 masu alaka da kashe-kashen gomman mutane a Benue a 2025.

    Sai dai sun musanta duka zarge-zargen bayan da aka karanta musu ta hanyar mai fassara.

    Babban lauyan gwamnatin ya buƙaci kotun da gajarta shari'ar tare da tsare waɗanda ake zargin har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar.

    Masu shigar da ƙarar sun ce tuni suka tanadi shaidu takwas da za su bayar da shaida a lokacin shari'ar.

    Kotun ta saka ranaku 26 da 27 ga watan Fabrairun da muke ciki domin ci gaba da shari'ar.

  11. An yanke wa tsohon ministan shari’ar China hukuncin ɗaurin rai da rai

    Wata kotu a China ta yanke wa tsohon ministan shari’a, Tang Yijin, hukuncin ɗaurin rai da rai bisa samunsa da karɓar rashawa.

    Kotar da ke lardin Fujian ta ce Tang ya karɓi wata kadara ba bisa ka’ida ba da darajarta ta kai kusan dala miliyan 20.

    Kotun ta kuma hana shi shiga harkokin siyasa har abada, tare da ƙwace dukiyarsa gaba ɗaya.

    Wannan hukunci na zuwa ne a yayin da Shugaban China, Xi Jinping, ke ci gaba da aiwatar da gagarumin yaƙi da cin hanci da rashawa, wanda ya sa a bincika ko hukunta manyan jami’ai da dama a ƙasar.

  12. Gobara ta laƙume shaguna a kasuwar Singa a jihar Kano

    ...

    Wata gobara da ta tashi a kasuwar Singa da sanyin safiyar Litinin ta haifar da gagarumar asarar dukiya, tare da jikkata mutane da dama.

    Rahotanni sun nuna cewa wutar ta tashi ne a rukunin shagunan Mazaf, inda ta ƙone kayayyaki masu yawa da har yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba.

    Bayanan sun ce gobarar ta auku ne da tsakar dare a kan titin Bello, cikin babbar kasuwar ta Singa. Har yanzu dai ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattara bayanai.

    Ɗan uwan mai mallakar rukunin shagunan da abin ya shafa, Barista Junaidu Muhammad Zakari,, ya bayyana irin barnar da gobarar ta yi.

    “Wutar ta yi mummunar barna sosai, ta ƙone kusan dukkan kayayyakin da ke cikin shagunan,” in ji shi. Sai dai ya ƙara da cewa, “Babbar sa’ar da muka yi ita ce wutar ba ta shafi makwaftan shaguna ba.”

    Shugaban kasuwar Singa da kewaye, Alhaji Musa Ibrahim Nabanki, ya ce an riga an fara gudanar da bincike kan lamarin.

    “Mun fara tattara bayanai domin gano abin da ya haddasa gobarar,” in ji Nabanki.

    ..

    A nasa bangaren, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce za su fara cikakken bincike da zarar an shawo kan sauran birbishin wutar.

    “Da zarar mun kammala kashe dukkan wutar gaba ɗaya, za mu fara bincike domin gano musabbabinta,” in ji shi.

    Bayanan da aka samu sun nuna cewa wannan ita ce gobara ta huɗu da ta auku cikin ƙasa da watanni uku a kasuwanni daban-daban na jihar Kano.

    Kasuwar Singa na ɗaya daga cikin manyan kasuwannin Kano, inda ake gudanar da hada-hadar kayan masarufi daga sassan Najeriya, har ma daga ƙasashen ketare.

    ...
  13. Ghana ta dakatar da tsarin bai wa ƴan ƙasar waje takardar zama ƴan Ghana

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Ghana ta dakatar da karɓar buƙatun neman zama ɗan ƙasa daga ƴan ƙasashen ƙetare.

    Wanna dakarwa ce ta wucin-gadi.

    Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida tare da Ofishin Harkokin mazauna ƙetare sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tsaftacewa da daidaitawa da kuma inganta tsarin neman zama ɗan ƙasa, wanda jami’an gwamnati suka amince cewa ya fuskanci ƙalubale a baya.

    Har yanzu ba a bayyana tsawon lokacin da dakatarwar za ta ɗauka ba, sai dai ana sa ran fitar da sabbin ƙa’idoji nan ba da jimawa ba.

    Duk da haka, akwai damuwa cewa wannan rashin tabbas na iya shafar tsare-tsaren wasu mazauna ƴan ƙasashen waje da ke alaƙanta kansu da Ghana, musamman waɗanda ke shirin yin zama na dogon lokaci ko zuba jari a ƙasar.

    Shirin bai wa ‘yan Afirka a faɗin duniya damar samun zama ƴan ƙasar Ghana ya samo asali ne daga tunanin masu son ƴancin Afrika bayan samun ‘yancin kai, wanda shugaban farko na ƙasar, Dr. Kwame Nkrumah, ya jagoranta.

  14. An kashe sojoji a musayar wuta da ƴanbindiga a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu dakarunta a wani babban farmaki da sojoji suka kai kan sansanin ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindiga a jihar Zamfara, inda ta ce ta yi wa ’yan bindigar mummunar asara.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan harin ’yan bindiga a ƙauyen Gwargwabe da ke yankin Nahuce a ƙaramar hukumar Bungudu, inda suka kashe mutum huɗu da suka haɗa da maza uku da mace ɗaya bayan al’ummar ƙauyen sun ƙi biyan harajin da ’yan bindigar suka nema.

    Rundunar ta ce sojojinta na Operation Fansan Yamma tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kai farmakin ne kan sansanin Gwaska Dan Karmi a ƙaramar hukumar Maru a ƙarshen mako bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan bindiga sama da 100 sun taru a wurin domin tsara hare-hare kan al’umma da hanyoyin jigilar kayan sojoji.

    Sojojinta sun gamu da matsananciyar turjiya, lamarin da ya haifar da fafatawa mai tsawo, kafin suka samu nasarar ƙwace sansanin tare da kashe ’yan bindiga da dama da kuma rusa sansanin.

    Duk da cewa ba a bayyana adadin ’yan bindigar da aka kashe ba, rundunar ta ce “da yawa” aka hallaka, tare da lalata makamai da cibiyoyin ajiyar kayayyaki.

    "Sai dai farmakin ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin jami'anmu tare da ƙona motar sojin guda ɗaya ta harin roka." in ji rundunar.

    Jihar Zamfara dai na daga cikin cibiyoyin rikicin ’yan bindiga a Najeriya, rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba al’umma da muhallansu a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

  15. An gurfanar da mutanen da ake zargin hannu a kisan gillar Yelwata

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Tarayya ta gabatar da wasu da ake zargi da hannu a kisan gillar Yelwata, jihar Benue, a gaban Kotun Tarayya, Abuja, a ranar Litinin, a gaban alƙali Joyce Abdul-Malik.

    Babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi ne ke jagorantar ƙarar kan mutum tara da ake tuhuma.

    Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa an gurfanar da su kan laifuka 57.

    A baya, ofishin babban lauyan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a tabbatar da adalci a wannan shari’a.

    “Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin kowa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji sanarwar Kamarudeen Ogundele, Mataimakin babban lauyan.

    Ogundele ya ce wannan mataki ya biyo bayan “bincike mai zurfi da hadin gwiwar hukumomin gwamnati.”

    A watan Yuni 2025 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari ga al’ummar Yelwata a ƙaramar hukumar Guma, jihar Benue, inda suka kashe mutane da dama tare da tilasta wa ɗaruruwa barin matsugunansu.

    Harin ya jawo zanga-zanga da suka karaɗe ƙasar da kuma suka daga ɓangarori da dama.

  16. An shirya kama ni a harbe ni a yunƙurin juyin mulkin da aka yi - Janar Musa

    ...

    Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa shi ma yana ɗaya daga cikin waɗanda ake hari a wani yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka shirya a watannin bayan inda ya ce;

    "Lokacin da wasu sojoji suka yi yunƙurin juyin mulki a Najeriya, an shirya kama ni kuma a harbe ni idan ban ba da haɗin kai ba."

    Janar Musa ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels inda ya tabbatar da cewa akwai shirin kashe shi a wani mataki na yunƙurin juyin mulki.

    Wannan bayani ya biyo bayan tabbacin da rundunar sojin ƙasar ta bayar game da yunƙurin, wanda aka kwashe watanni ana yaɗa jita-jita a kansa.

    “Ni ma ina cikin waɗanda ake hari a yunƙurin juyin mulkin da aka yi,” in ji tsohon Shugaban Sojin Najeriya mai ritaya.

    A watan Oktoba, rundunar soji ta kama sojoji 16 kan “aiki da rashin ladabi da ƙeta dokokin aikin soja.”

    Amma bincike ya nuna cewa wasu daga cikin waɗannan sojojin suna da hannu a shirin kifar da gwamnati Tinubu, abin da ya saba wa ƙa’idojin aikin soja.

  17. Falasɗinawa sun fara tsallaka iyakar Rafah bayan shekar biyu a rufe

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Falasɗinawa sun fara tsallaka iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar, bayan an sake buɗe ta saboda shige da ficen Falasɗinawa da kuma jigilar kayan agaji.

    Mashigar ta kasance a rufe kusan shekara biyu bayan da sojojin Isra'ila suka ƙwace ɓangaren yankin Gaza..

    Sake buɗe mashigar Rafah wani muhimmin ɓangare ne a yarjejeniyar tsagaita wuta ta shugaba Trump a Gaza.

    Ana ƙiyasin cewa kusan Falasɗinawa 20,000 da suka jikkata ko ke buƙatar magani suna jiran fita daga Gaza don samun kulawa.

    Rahotannin Isra’ila sun nuna cewa, marasa lafiya 50 da masu jinyarsu biyu ne za a bari su tsallaka mashigar a kowace rana.

    Mashigar za ta kasance karkashin kulawar jami’an Tarayyar Turai da ma’aikatan Falasɗinawa na cikin gida, yayin da Isra’ila za ta gudanar da binciken tsaro daga nesa.

  18. Yadda maciji ya kashe matashiyar mawaƙiya ƴar Najeriya a Abuja

    ...

    Asalin hoton, Ifunanya Nwangene / Instagram

    An shiga jimami a Najeriya bayan rasuwar matashiyar mawaƙiya mai tasowa, Ifunanya Nwangene, mai shekara 26, wadda ta mutu a ranar Asabar bayan maciji ya sare ta a gidanta da ke Abuja.

    Ifunanya ta shahara ne bayan bayyanar ta a gasar “The Voice Nigeria” a 2021, inda ta ja hankalin jama’a da ƙwarewarta a waƙa.

    Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ake fitar da macijin daga gidanta, yayin da ake jin mutane na ihu suna cewa, “kumurcin maciji ne!”

    Wani abokinta na kusa, Sam Ezugwu, wanda ya kafa ƙungiyar Amemuso Choir, ya shaida wa BBC cewa Ifunanya “ta kasance tauraruwa mai tasowa” kuma tana ƙoƙarin fitar da waƙoƙinta na farko a wannan shekarar.

    Wani abokinta kuma, Hillary Obinna, ya ce an sanar da shi cewa tana barci ne lokacin da macijin ya sare ta inda ya ƙara da cewa “daga bisani an gano macizai biyu a cikin gidan.”

    Ya ce an fara kai ta wani asibitin kusa da gidanta ne amma suka ce ba su da maganin cizon maciji, kafin daga bisani aka kai ta asibitin gwamnatin tarayya, wato Federal Medical Centre da ke Jabi.

    Sai dai an samu saɓani kan batun magani, inda ya ƙara da cewa “da aka kai ta asibitin ta unguwar Jabi, an samu maganin maciji guda ɗaya, alhali biyu ake buƙata,” amma kuma asibitin ya musanta hakan, yana mai cewa an ba ta kulawa ta gaggawa da allurar maganin cizon maciji."

    Asibitin ya ƙara da cewa, "Da yake yanayin halin da take ciki ya tsananta sakamakon illar sarar macijin, kuma likitocinmu sun yi bakin ƙoƙarinsu amma sun kasa ceton rayuwarta,” lamarin da ya sake tayar da muhawara kan ingancin kiwon lafiya da kulawa da marasa lafiya a Najeriya.

  19. Zelensky ya yi allawadai da harin bas daga Rasha da ya kashe mutum 12

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi allawadai da mummunan harin da Rasha ta kai kan wata motar bas da ke ɗauke da masu haƙar ma'adinai inda ya kira shi a matsayin tsantsar zalunci.

    Ya ce harin ya nuna ƙarara cewa Rasha na ruruta wutar faɗan yaƙin da suke yi a tsakaninsu.

    Aƙalla mutum 12 ne suka rasa ransu yayin da wasu 16 kuma suka samu rauni a harin wanda aka kai a yankin Dnipropetrovsk.

    Jami'an Ukraine sun ce an kai harin ne da jirgi maras matuki.

    Hotunan harin sun nuna tarkacen motar da tagogin bas din duk sun fashe sannan kuma ga gawar mutane a kasa.

    An kai harin ne gabanin jawabin da shugaba Zelensky ya yi cewa za a koma domin ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da Rasha da kuma Amurka a Abu Dhabi a ranar Laraba mai zuwa.

  20. Sheikh Usman Kusfa Zaria ya rasu

    Sheikh Usman Kusfa Rigirigi

    Asalin hoton, Sheikh Usman Kusfa Rigirigi/Facebook

    Allah ya yi wa Sheikh Usman Kusfa Zaria, wanda aka fi sani da Rigi-rigi rasuwa a daren jiya Lahadi a jihar Kaduna.

    Fitaccen malamin ya rasu ne bayan fama da gajeriyar jinya, sannan ya rasu ne a asibitin sojojin Najeriya na 44 da ke ke Kaduna.

    Malamin ya rasu ne yana da shekara 57, kuma ya rasu ya bar matansa huɗu da ƴaya 37.

    Sheikh Usman ɗan asalin garin Kusfa ne da ke Zaria a jihar Kaduna.