BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, 'Ba za mu taɓa yafe wa waɗanda suka kashe ƴan Shi'a ba a Zaria'
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2025.
Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da Saudiyya, wane alfanu za ta samu?
A ranar Laraba ne ƙasashen biyu suka saka hannu kan yarjejeniyar domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro da ayyukan soja tsakaninsu.
Yadda kisan mata a Adamawa ke jan hankali a Najeriya
''Abin da jama'a suka tabbatar mana shi ne cewa wani soja ne ya buɗe wuta ya yi sanadiyyar wannan asarar rayuka da aka yi.''
Shin Birtaniya za ta iya jure yaƙi mai tsawo da Rasha?
A Birtaniya, manyan hafsoshin tsaro sun yi gargaɗin cewa idan suna so su guje wa yaƙi, dole su fara shirin yaƙin. Amma idan yaƙin ya ɓarke da Rasha, shin Birtaniya za ta jure ko da mako ɗaya tana yaƙin?
Bidiyo, Daga Bakin Mai Ita tare da Al-amin Buhari, Tsawon lokaci 5,57
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Al-amin Buhari, shahararren ɗanwasan kwaikwayo a Kannywood.
Ko Tinubu ya karya dokar Najeriya ta hanyar tura sojoji Benin?
A wani saƙo da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta ce bisa umarnin Shugaba Tinubu jiragen yakin Najeriya suka karɓe iko da sararin samaniyar Jamhuriyar Benin ranar Lahadi domin daƙile yunƙurin masu son yin juyin mulki.
Sojojin Najeriya sun kashe na hannun damar Turji, Kachalla Kallamu a Sokoto
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/12/2025.
Ko zai yiwu a hana yara amfani da shafukan sada zumunta?
Daga ranar 10 ga Disamba ne dokar haramcin amfani da shafukan sada zumunta ga yara ƴan ƙasa da shekara a 16 Australia ta fara aiki.
Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci
Daga alƙaluma na baya-baya da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar, kimanin kashi 30.9% na al'ummar Najeriya ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci, a cewar Bankin Duniya.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Rana, 13:59, 11 Disamba 2025, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 11 Disamba 2025, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 11 Disamba 2025, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 10 Disamba 2025, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Wasanni
City ta ƙara nuna ɓarakar Real Madrid, Arsenal ta ci gaba da jan zarenta
Wannan rashin nasara da Real Madrid ta yi a gida ya ƙara ɗora ayar tambaya kan makomar koci Xabi Alonso a ƙungiyar.
KAI TSAYE, Pogba ya zama jakadan tseren rakuma ya kuma sa hannun jari a wasan
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 5 zuwa 5 12 ga watan Disambar 2025.
Man United na zawarcin Ramos Sunderland na son Guendouzi
Man United na zawarcin tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 39,wanda ya bar Monterrey ta Mexico, yayin da Sunderland ke son tsohon ɗan wasan Arsenal da Faransa Guendouzi.
Ko akwai wani abu da ya rage wa Salah a Liverpool?
A yammacin ranar Asabar Salah ya ba mutane da dama mamaki lokacin da ya sanar da ’yan jarida cewa alakarsa da mai horaswa Arne Slot “ta lalace”.
Sakamakon wasannin Champions League na ranar Talata
Har yanzu Arsenal ce ta farko a kan teburi da maki 15 daga karawa biyar, duk da nasarar da Bayern Munich ta yi kan Sporting da ci 3-1, inda ƙwallaye suka raba ƙungiyoyin biyu na saman teburi.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Nzeogwu Kaduna: Sojan da ya fara kitsa juyin mulki a Najeriya
Abokansa ƴan arewa ne suka raɗa masa suna Kaduna kasancewar a nan ne aka haife shi sannan kuma yana jin harshen Hausa kamar jakin Kano fiye da harshensa na Igbo.
Wace rawa sojojin Najeriya da Tinubu ya aika Benin za su taka?
Shugaba Tinubu ya yi gargaɗin cewa Jamhuriyar Benin na fuskantar "yunƙurin ƙwace mulki ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar ruguza cibiyoyin dimokuraɗiyya".
Me ya sa jirgin sojin Najeriya ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso?
Sanarwar AES ta ce binciken hukumomin Burkina Faso ya tabbatar da cewa jirgin samfurin C-130 na Najeriya ya shiga kasar ba tare da izini ba kuma yana ɗauke da mutum 11.
Fubara ko Wike: Da wa Tinubu zai fi ɗasawa?
Masana na ganin sauya sheƙar Fubara tamkar wani yankan baya ne ga tsohon ubangidansa, kuma ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, Nyesom Wike, da suka dade suna samun takun saka tsakaninsu, kasancewar a yanzu Fubara ne zai ci gaba da jan ragamar jam'iyyar APCn jihar.
Gwamnan jihar Rivers, Fubara ya sauya sheƙa zuwa APC
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Jamal Gamal Abdel Nasseer: Mutumin da ya fara juyin mulki a Afirka
Ƙididdiga ta nuna cewa daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka 54, 45 daga ciki sun fuskanci juyin mulki ko da sau ɗaya ne.
Yanayin da ƙasar Syria ke ciki shekara ɗaya bayan hamɓarar da gwamnatin Assad
Shekara guda da fara mulkinsa Shugaban Syria ya yi nasarar zawarcin Trump da kuma yawancin ƙasashen yammacin duniya, amma a cikin gida mutane sun san rauninsa
Lokuta biyar da Najeriya ta kai ɗaukin soji a wasu ƙasashen Afirka
Sojojin sun hanzarta wajen mayar da martani kan buƙatar da gwamnatin Benin ta miƙa ta ceto dimokuraɗiyyar ta shekara 35, in ji Tinubu a wata sanarwa da ya fitar.
Gwamnatin jihar Neja ta karbi ɗalibai 100 da aka ceto
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/12/2025.
Ko ya kamata Najeriya ta hada kai da Faransa kan matsalar tsaro?
Sai dai a daidai lokacin da ake tunanin yadda za ta kaya kan barazanar ta Trump ne sai kallo ya koma sama bayan Faransa ta miƙa tayin za ta iya haɗa hannu da Najeriya domin magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Fitar da ɗantakarar gwamna a Kano a APC a yanzu zai haifar da rarrabuwar kai — Ganduje
Ganduje ya ce fitar da dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a Kano yanzu, ba dai-dai bane
Yadda aka kafa Isra'ila a tsakiyar Larabawa da tsagin yankin Falasɗinawa
Isra'ila, wadda aka kafa shekaru 75 da suka wuce ta zamo mai ƙarfin faɗa a ji, a yankin, yayin da Falasɗinawa ke ci gaba da neman mafaka a ƙasashen waje kuma sun kasa kafa tasu ƙasar mai zaman kanta.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.




































































