Halin da mummunan tunani zai iya jefa ku a ciki

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Yasmin Rufo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Shin ka taɓa shiga wani yanayi mai muni, har ka yi tunanin ka kwarma ihu? ko kuma kana tsaka da tuƙin abin hawa, wani mummunan ''tunanin hatsari'' ya zo maka?
Wannan yanayi maras kyau shi ake kira ''munanan tunane-tunane'', wanda mafi yawanmu ke fuskanta lokaci zuwa lokaci.
To amma ga wasu lamarin na yin muni, su gaza fita daga cikinsa har ma yana iya haifar musu da wasu ɗabi'u.
A lokacin da Dokta Nina Higson-Sweeney ke ƙarama, wani abu a ranta na ce mata in dai ba ta yi tunanin abubuwa masu kyau ba a hanyarta ta zuwa gida, daga makaranta, to lallai wani mummunam abu zai faru da danginta.
"Da zarar na yi wani mummunan tunani, sai na koma na sake faro tafiyar daga tashar mota," in ji ta. "Na shiga cikin mummunan firgici, kan cewa idan ban sake tafiyar ba daga farko, kuma wani mummunan abu ya faru da iyalina, to laifina ne.”
A lokacin da Nina ke da shekara 10 likitoci sun gano tana ɗauke da matsalar OCD (ɗabi'ar da ke tursasa mutum yin wani abu).
A yanzu haka Nina na aiki a matsayin mai binciken ilimin tunanin ɗan'adam Jami'ar Oxford da ke Birtaniya inda ta ƙware a fannin lafiyar ƙwaƙwalwar yara da manya.

Asalin hoton, Dr Nina Higson-Sweeney
"Munanan tunani wasu tunane-tunane marasa kan gado da ke zo wa mutum da a wasu lokuta ke tilasta wa mutum yin wasu abubuwa ko maimaita su, ko haifar da yin wasu munanan abubuwa domin kawar da damuwar da tunane-tunanen ke haifarwa,'' kamar yadda Nina ta shaida wa BBC.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tunane-tunanen kan iya zama munana da wasu lokutan ke janyo wani yanayi da ya saɓa da hallaya ko ɗabi'ar mutum.
"Za ka iya tunanin wani mummunan abu ya faru da masoyinka,'' in ji Nina.
"Har ma yakan shafi sha'awar jima'i, da zai sa a wani lokaci ka yi tunanin kai mai son jinsi ne ko kishiyar jinsinka, kai har ma wani lokaci ka ji ji sha'awar ƙananan yara''.
"Abin da ya fi yawa game da matsalar shi ne tunanin da ke shiga tsakani game da gurɓatawa da kuma damuwa game da rashin lafiya ko yaɗa cuta," in ji ta.
Galibi lalurar OCD kan fara ne a lokacin da mutum ya fara balaga, amma wasu mutane akan gano suna ɗauke da lalurar ne bayan sun fara girma,'' in ji Nina.
Bincike ya gano cewa wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da lalaurar sun hada da yanayi da mutum ya gamu da shi tun yana yaro, kamar cin zali da jimami da kuma rabuwar iyali.
Ƙwararriya a fannin tunanin ɗan'adam, Kimberley Wilson ya ce kusan kowa ya taɓa fuskantar lalurar OCD a wasu lokuta.
"Bincike ya nuna cewa kusan kashi 80 na mutane na da wannan lalura," kamar yadda ta yi ƙarin haske.
Ga mutane da dama waɗannan tunane-tunane kan zo kuma su wuce da sauri.
"A wasu lokuta idan muka yi tunanin, mukan ɗauke su a matsayin ban mamaki, sannan mu manta da su," in ji ta.
Idan ba ma iya mantawa da su, to a nan ne muke buƙatar taimako, a cewarta.
"Tunane-tunane masu alaƙa da lalurar OCD ba sa wucewa, sukan riƙa zuwa a kai a kai, kuma a koyaushe ba su zama masu kyau, tunani ne da ke harzuƙa mutum, kuma idan har ba a iya kauce musu, a lokacin ne suke zama hatsari, har su haifar da tursasa wa mutum aikata mummunan abu.''
Alamomin tursasawa ka iya zama na ƙwaƙwalwa, kamar ƙirge zuwa wasu lambobi, ko yawaita kallon wasu abubuwa, kamar yawaita duba tayoyin mota, duk kuwa da cewa ba su da wata matsala.
Yaya za ku rayu da lalurar OCD?
A wannan yanayi "Ƙwararru ne kawai za su iya ba ku shawarwarin yadda za ku yi,'' in ji Nina.
Baya ga taimakon ƙwararru, Nina ta ce akwai wasu dabaru da mutane za su iya amfani da su da za su taiamaka wajen raguwar kaifin matsalar.
Ɗaya daga ciki shi ne ka fahimci kana da matsalar. ''Fahimtar kana da lalurar OCD na taimakawa wajen rage maka kaifin lalurar, ta yadda idan tunanin ya zo maka za ka yi saurin tunawa da ita,'' in ji ta.
Wasu mutanen kan taimaki kansu ta hanyar ɗaukar lalurar OCD a matsayin wata baƙuwar ɗabi'a da ke zuwa musu.
"Sanya shamaki tsakaninka da lalurar, ta yadda za ka iya bambance tunaninka da na OCD idan ya zo zai taimaka maka''.
Haka ma kula da kai na taimakawa.
"Cin abinci mai kyau da samun isassashen hutu da motsa jiki kai taimaka wa mai lalurar OCD, saboda a lokacin gajiya da damuwa ne ba za ka iya kula da kanka ba'', kamar yadda ta bayyana.
A yau Nina na rayuwa da lalurar OCD amma ta koyi yadda za ta tafiyar da ita.
"Ban taɓa rabuwa da lalurar OCD ba, amma na koyi yadda zan tafiyar da ita. Nakan yi munanan tunane-tunane amma na san zan warware su. Idan ina cikin gajiya nakan sha wahala kafin na iya warware munanan tuane-tunanen kuma a wasu lokutan sukan tursasamin yin abubuwan da ba su dace ba.''










